Cutar Anthrax: Jihar Legas ta Kashe wasu Dabbobi shida da suka kamu da cutar
Maimuna Kassim Tukur,Abuja.
Gwamnatin jihar Legas ta ce ta kwace, ta kona tare da binne wasu dabbobi shida da suka kamu da cutar Anthrax, domin hana yaduwa.
Sakatariyar dindindin ta ma’aikatar noma, Misis Olatokunbo Emokpae ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi.
Misis Emokpae ta ce; “An gano wadanda suka kamu da cutar ne yayin da ake sa ido kan dabbobi a tsibirin Legas da Agege.”
Emokpae ya ce “ba a gano ko kuma an samu rahoton bullar cutar ba tun lokacin da aka gano cutar Anthrax a Legas.”
Ta ce an kara kaimi wajen sa ido kan mutane da dabbobi.
A cewarta, “an kara yawan ayyukan rigakafi da sa ido.”
Misis Emokpae ta ce; “Masu dabbobi su yi amfani da wannan atisayen ta hanyar zuwa da garken su domin yi musu allura.
“Don Allah a ba da rahoton alamun cutar dabbobi ga Daraktan Ma’aikatar Aikin Noma ta Jihar Legas ta wayar tarho 08023427594, 08180703010 ko kuma a tuntubi likitan dabbobi ta 08023328244.”
Maimuna Kassim Tukur.
Leave a Reply