Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Zai Yiwa ‘Yan Najeriya Jawabi A Kafafn Watsa Labarai Na Kasa

0 120

Shugaba Bola Tinubu zai yi wa al’ummar kasar jawabi a ranar Litinin, 31 ga Yuli, 2023 da karfe 18:00 agogon GMT.

 

Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake ne ya bayyana hakan a wani sako da ya fitar a safiyar ranar Litinin.

 

Ya kuma bukaci gidajen talabijin da rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su hada kai da ayyukan sadarwar Hukumar Talabijin ta Najeriya da Rediyon Najeriya domin yada shirye-shiryen.

 

Ana sa ran watsa shirye-shiryen za su tabo kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta a halin yanzu musamman ma mugunyar illar cire tallafin da ake yi wa Premium Motor Spirit (PMS) da aka fi sani da fetur.

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *