Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Neja Ya Bukaci Hukumar N-HYPPADEC Ta Kara Himma A Ayyukan Ta

Nura Muhammed,Minna.

0 152

Gwamnan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Umar Mohammed Bago ya bukaci hukumar dake samar da cigaba ga jahohin dake samar da wutan lantarki ta ruwa wato N-HYPPADEC da su kara kokari wajan cimma kudirin su na aiwatar da ayyukan cigaba ga jahohin dake karkashin kulawar su.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar Shugabannin hukumar suka ziyarci shi a gidan gwamnati dake Minna fadar gwamnatin jihar, inda ya ci kaso 32 da jihar Neja ke samu daga ayyukan ta sun yi kadan

 

 

Har ila yau gwamna Umar Mohammed Bago ya kara da cewar gwamnatin jihar zata hada hannu da hukumar ta N-HYPPADEC don ganin alummar jihar sun anfana da ayyukan ta, duba ga yadda jihar ta kasance kan gaba da manya manyan Dam Hudu da ake Samar da wutan lantarki a kasar.

 

Gwamnan ya kuma ce akwai bukatar ganin an wayar da kan alumma don sanin yadda zasu bi wajan kaucewa shiga hadarin ambaliyar ruwa, da Kuma yadda za a gyra magudanar ruwa, ta yadda za a cimma biyan bukata.

 

” A fadakar da alumma sanin yadda zasu kare kansu da Kuma dukiyoyin su daga ambaliyar ruwa, kuma ya kasance hakan na tafiya da kudirin gwamnatin jihar Neja, musamma wajan tsara ayyukan cigaba ga alummar, ya kasance hukumar ta hada kai da gwamnatin jihar don kada a sami  rashin fahimtar juna wajan gudanar da ayyukan cigaba ga alummar” inji Gwamna Umar Mohammed Bago.

 

Tun da farko a jawabin sa Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Sadiq Yalwa ya yabawa Gwamnan jihar wajan biyan nasu kason ga hukumar da kuma yadda ake samun fahimtar juna a tsakanin hukumar da gwamnatin jihar Neja.

 

Sadiq Yalwa ya bayyana cewar an sake sauyawa hukumar sunan ta izuwa N-HYPPADEC wato National -Hydro Power Producing Area Development Commission, inda ya ce an sami karin wasu jahohi 4 da suka hada da Gombe da Taraba da Nasarawa da kuma jihar Kaduna da suka shiga jerin jahohin dake karkashin kulawar hukumar, wanda kuma jihar Neja ce kan gaba da yawan kananana hukumomi da suka kai 17, inda ake da ofishin yanki 3 da ya hada da New Bussa da Gwada da kuma Bida.

 

 

Nura Muhammed.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *