Take a fresh look at your lifestyle.

Birtaniya Ta Shirya Don Bin Sahun Afirka Ta Yamma A Kokarin Dawo Da Dimokuradiyya A Nijar

0 126

Birtaniya da kawayenta a shirye suke su goyi bayan duk wani yunkurin da shugabannin kungiyar Ecowas za su yi na maido da dimokuradiyya a Nijar, inda a kwanan nan aka hambarar da shugaban a wani juyin mulki, in ji sakataren harkokin wajen Birtaniya James Cleverly.

Da yake zantawa da BBC a birnin Accra, Mista Cleverly ya ce yana da muhimmanci shugabannin Afirka su jajirce wajen mayar da martani, kuma idan Birtaniya ta samu takamaiman bukatu na taimako za ta yi la’akari da su.

Shugabannin yankin da kasashen yamma sun yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar tare da sanyawa kasar takunkumi. Amma sojojin da ke kula da Mali da Burkina Faso ba su amince da wannan matakin ba.

A ranar Litinin ne Birtaniya ta sanar da dakatar da tallafin da take baiwa Nijar, sai dai Mista Cleverly bai bayyana wani takunkumin da aka sanyawa wadanda suka yi juyin mulki ba.

Da aka tambaye shi game da fadada rukunin Wagner na Rasha a Afirka, Ministan Harkokin Wajen Burtaniya ya bayyana cewa Vladimir Putin da kungiyar Wagner ba abokan al’ummar Afirka ba ne saboda yadda suke cin gajiyar ayyukansu.

A halin da ake ciki, Birtaniya na da burin zama abokiyar kawance a nahiyar, in ji Mista Cleverly.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *