Yanzu haka ana shirin fara wani taro na musamman na Hukumar Shugabannin Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne zai jagoranci taron, wanda a halin yanzu ke jagorantar kungiyar ta yankin.
Shugabanni da shugabannin gwamnatocin kasashen yankin yammacin Afirka na halartar taron.
Shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Tinubu ne ya kira taron a ranar Litinin, domin yin nazari kan matakan da za a dauka na maido da mulkin dimokradiyya a Jamhuriyar Nijar.
Nijar ta fuskanci juyin mulki a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, lokacin da jami’an tsaron fadar shugaban kasar suka tsige shugaban kasar, Mohammed Bazoum.
Kungiyar ECOWAS ta mayar da martani inda ta kakabawa Nijar takunkumi, inda ta dage kan cewa dole ne a maido da Bazoum, inda ta bada wa’adin kwanaki bakwai, wanda ya kare a ranar Lahadi 6 ga watan Agusta amma masu yunkurin juyin mulkin sun dage.
Yanzu dai duk duniya na jiran shawarwarin da za su fito daga taron na yau, da fatan cimma matsaya da masu yunkurin juyin mulkin.
Leave a Reply