Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Yobe Ta Bukaci Kananan Hukumomi Da Su Fadakar Kan Rigakafin Ambaliyar Ruwa

0 200

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya bukaci hukumomin kananan hukumomi da su wayar da kan jama’a kan illolin ambaliya da kuma muhimmancin bin matakan gargadin gaggawa a matsayin wani shiri na dogon lokaci.

 

Buni ya bayyana haka ne a wani taron bita kan shirye-shiryen bala’o’in ambaliyar ruwa da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta shirya, tare da bayar da tallafi daga kungiyar Samar Kyakyawan Yanayin Harkokin Gona (ACReSAL).

 

Ya kuma bukaci shugabannin al’umma da su dauki matakan kariya don share yashi da magudanan ruwa da suka toshe don gujewa ambaliya.

 

Buni, wanda Baba Malam-Wali ya wakilta, ya ce makasudin gudanar da taron shi ne inganta shirin jihar da kuma mayar da martani ga yiwuwar ambaliyar ruwa bisa hasashen NiMet.

 

Har ila yau, Dokta Mohammed Goje, Babban Sakatare na SEMA, ya bayyana cewa, gogewar ambaliyar ruwa a shekarar 2022 ya gwada karfin hukumar ta fuskar shirye-shirye, ragewa, da kuma mayar da martani.

 

Ya bayyana cewa, an yi asarar rayuka da dama, an kwashe matsugunai da gonaki, an kuma katse hanyoyi, wanda hakan ya sa hukumar ta kai agaji ga wasu da abin ya shafa.

 

A cewarsa bisa la’akari da abubuwan da suka faru a baya, Buni ya umurci hukumar da ta samar da wani tsari don gujewa irin wannan kwarewa.

 

Ko’odinetan ayyukan ACReSAL, Alhaji Shehu Mohammed ya yabawa SEMA bisa shirya taron, inda ya bayyana shi a matsayin taron da aka yi a kan lokaci.

 

 

Ya kuma bayyana wasu ayyuka da yawa na ACRESAL don rage tasirin sauyin yanayi a jihar.

 

 

 

NAN / Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *