Shugaban sojojin Mali, Assimi Goita, ya bayyana cewa kwanan nan ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan halin da ake ciki a Nijar.
Jamhuriyar Nijar dai ta fuskanci juyin mulkin da sojoji suka yi, lamarin da ya janyo damuwa a kasashen duniya.
A cikin wani sako da aka watsa a dandalin sada zumunta na X (tsohon Twitter), Goita ya bayyana cewa, Putin ya jaddada muhimmancin kudurin lumana don tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel.
Kasashen yammacin duniya na fargabar cewa Nijar na iya bin tafarkin Mali, inda a baya aka yi juyin mulkin da ya kai ga shigar sojojin haya na kungiyar Wagner ta Rasha a yunkurin da ake yi na yakar ‘yan tawaye.
Putin ya bukaci a maido da tsarin mulki a Nijar, a daya bangaren kuma shugaban kungiyar Wagner Yevgeny Prigozhin ya nuna goyon bayansa ga juyin mulkin.
Wani abin sha’awa dai shi ne, an samu gagarumin rinjaye na goyon bayan Rasha a Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar, inda magoya bayan gwamnatin mulkin sojan kasar suka daga tutocin kasar ta Rasha.
Africanews/Ladan Nasidi.
Leave a Reply