Take a fresh look at your lifestyle.

Nijar ta yi asarar sojoji 17 a wani hari da aka kai kusa da iyakar Mali

0 102

Akalla sojojin Nijar 17 ne suka mutu yayin da 20 suka jikkata sakamakon wani hari da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai a kusa da kan iyakar Nijar da Mali, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar a birnin Yamai.

 

Da yammacin ranar Talata, “wani bangare na rundunar sojojin Nijar (FAN) da ke tafiya a tsakanin Boni da Torodi sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna a kusa da garin Koutougu,” a cewar wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a yammacin ranar Talata.

 

Ya kara da cewa, an kashe sojoji 17 tare da raunata 20, shida daga cikinsu sunji munanan raunuka, “dukkan su an kwashe su zuwa Yamai”, in ji shi, yana mai bayyana cewa “har yanzu ana ci gaba da aikin ceto”.

 

Sojojin sun tabbatar da cewa a bangaren maharan, “guda biyu na babura sama da hamsin kowanne” sun “lalata kayan su kuma sama da ‘yan ta’adda dari ne aka kashe a lokacin da suka janye”.

 

Yankin Koutougu yana kusa da iyakar Mali a yankin Tillabéri (kudu maso yamma).

 

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka sani tun bayan juyin mulkin ranar 27 ga watan Yuli a Nijar wanda ya hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

 

Sojojin da suka karbi mulki karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani, sun gabatar da “tabarbarewar yanayin tsaro” don tabbatar da juyin mulkin da suka yi.

 

Yankin Tillabéri yana cikin yankin da ake kira “iyakoki uku” tsakanin Nijar, Burkina Faso, da Mali, kuma mafaka ce ta ‘yan ta’adda.

 

Shekaru da dama, wannan yanki na Nijar ya sha fama da hare-hare daga wadannan kungiyoyi masu dauke da makamai duk da dimbin dakarun da ke yaki da ta’addanci.

 

Kafin juyin mulkin, kasar Faransa wadda tsohuwar mulkin mallaka ce da ke da sojoji 1,500 a Nijar, tana da hannu dumu-dumu da sojojin Nijar wajen yakar wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

 

Sabuwar gwamnatin mulkin soja a Yamai ta dauki Faransa a matsayin babbar manufarta, inda ta zarge ta da son tsoma baki ta hanyar soji domin mayar da shugaba Bazoum kan aikinsa.

 

 

Africanews/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *