Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta gudanar da wani shirin horaswa ga matan Najeriya, da nufin samar musu da muhimman fasahohin da suka wajaba don shiga cikin nasara a harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka.
Taron mai taken “Ginawa Kungiyar ‘Yan Kasuwa Ta Yamma Akan Samun Kasuwar Yanki da Nahiyar A karkashin tsarin Cinikayya” an gudanar da shi kwanan nan a Legas.
A jawabinta na maraba, shugabar kungiyar ECOWAS ta ‘yan kasuwar Alaba Lawson, ta ce, “babban makasudin wannan taron shi ne tabbatar da shigar da mata daga yankin ECOWAS cikin yankin ciniki maras shinge na nahiyar Afirka, don samar da sauki ga kayan mu.
“Yana da matukar muhimmanci mu hada kai mu magance duk wani kalubalen da ya taso tare da sanya kanmu kan dabarun gaba na sauran yankuna dangane da shiga AFCFTA.”
Har ila yau, mai ba da shawara kan harkokin kasuwanci da kamfanoni masu zaman kansu na Deutsche Gesellschaft fur Internationale Zusammenarbeit, Raymond Dagana, ya ce, “Manufar Shirin Gudanar da Ciniki a Yammacin Afirka shi ne bunkasa kasuwancin yanki da na duniya maras cikas ta hanyar rage lokaci da tsadar kayayyaki. Yana ba da haɗin kai sosai tare da masu ruwa da tsaki don sauƙaƙa tsarin rajistar kasuwanci da takardun tabbatar da ingantaccin kaya. ”
A nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas, Wale Cole, ya bayyana cewa, AFCFTA ita ce yankin ciniki cikin ‘yanci mafi girma a duniya, inda ya hada kasashe 55 na kungiyar Tarayyar Afirka da kuma al’ummomin tattalin arzikin yankin.
A cewarsa, gaba daya aikin hukumar ta AFCFTA shi ne samar da kasuwar nahiyar guda daya mai yawan al’umma biliyan 1.3 sannan kuma tare da hadakar kayayyakin cikin gida da ya kai kusan dala tiriliyan 34.
Cole ya ce, “Wannan yarjejeniya ba za ta yi tasiri ba sai dai idan ‘yan Afirka sun jajirce sosai. Kasashen da ke wajen Afirka da suka ga mun dogara da su kuma suka ga mu masu ciyar da su da tattalin arzikinsu ba za su so wannan yarjejeniya ta yi aiki ba.”
A halin da ake ciki, ya yabawa shugabannin Afirka da suka fara yarjejeniyar kasuwanci.
Ya jaddada cewa sadaukarwa na da mahimmanci don samun nasara.
Cole ya kara da cewa kasashen waje ba za su goyi bayansa gaba daya ba saboda zai rage dogaro.
Ya yi nuni da yarjejeniyoyin kasuwanci na shiyya-shiyya da na nahiya, yana mai jaddada bukatar su ma su sanar da kamfanoni masu zaman kansu.
Punch/Ladan Nasidi.
Leave a Reply