Take a fresh look at your lifestyle.

Dakarun Yammacin Afirka Za Su Yi Zaman Tattauna Matsalolin Nijar

0 153

A yau Juma’a ne shugabannin sojojin kasashen yammacin Afirka za su yi zaman tattaunawa a rana ta biyu kuma ta karshe a birnin Accra na kasar Ghana, inda suke ta tofa albarkacin bakinsu kan yuwuwar tsoma bakin soja a Nijar, idan har diflomasiyya ta kasa ta kawo karshen juyin mulkin da sojoji suka yi.

 

Jami’an soji sun hambarar da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, kuma sun yi fatali da kiraye-kirayen Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar ECOWAS da sauran kasashen Afirka ta Yamma na a maido da shi bakin aiki, lamarin da ya sa kasashen yankin suka ba da umarnin a kafa rundunar tsaro.

 

A yayin ganawar tasu ta kwanaki biyu, wacce aka kammala da bikin rufewa daga da misalin karfe 1600 agogon GMT, hafsoshin tsaron sun tattauna kan dabaru da sauran abubuwan da za a iya turawa, kamar yadda jadawalin hukuma ya nuna.

 

Yin amfani da karfi ya kasance mataki na karshe, amma “idan komai ya gaza, dakarun da ke yammacin Afirka… a shirye suke su amsa kiran aiki,” in ji kwamishinan siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS Abdel-Fatau Musah a wurin taron a ranar Alhamis.

 

Ya ce akasarin kasashe 15 na kungiyar a shirye suke su shiga cikin rundunar tsaro, in ban da wadanda suke karkashin mulkin soja – Mali, Burkina Faso da Guinea da kuma Cape Verde.

 

Duk wani tashin hankali zai kara dagula zaman lafiya a yankin Sahel na yammacin Afirka, wanda tuni ke fama da tashe tashen hankula da aka kwashe shekaru goma ana yi.

 

Ita ma Nijar tana da muhimmiyar dabara fiye da Afirka ta Yamma saboda ma’adinin Uranium da man fetur da kuma rawar da take takawa a matsayin cibiyar sojojin kasashen waje da ke da hannu wajen yaki da masu tada kayar baya.

 

 

Reuters/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *