Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Neja Zata Farfado Da Bangaran Yawon Bude Ido.

By: Nura Mohammed. Minna, Niger State.

0 244

A kokarin ta na inganta bangaran al’adu da yawon bude ido, Gwamnatin Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta dauki aniyar farfado da cibiyar kiwon Kaji dake Suleja, wato Dr Ladi Kwali Pottery center domin inganta sashen bisa tsari da kuma kudirin bankin duniya na farfado da cibiyoyin da kuma inganta su.

Bisa wannan kudirin ne babban sakatare a Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido na jihar, Dr Idiris Legbo ya ziyarci cibiyar dake Suleja domin ganin yadda ayyukan ke tafiya a cibiyar don ganin sun dace da tanaje tanajen gwamnatin jihar.

Dr Idiris Legbo ya kara da cewar, gwamnan jihar Neja Umar Mohammed Bago a shirye yake ya farfado da bangaran yawon bude ido, da kuma samar da cikakkiyar kulawa a cibiyoyin ta yadda zasu bada gudumuwa na samarwa da jihar kudaden shiga.

 

Babban sakataran ya kuma jaddada kudirin gwamnatin na cigaba da lalibo hanyoyin da zasu kai ga samar da cigaba a bangaran yawon bude ido, ganin irin mahimmancin dake tattare da su.

Da yake zagayewa cibiyar, Dr Idiris Legbo ya ce da zarar an Kammala ayyuka a cibiyar na Dr Ladi Kwali Pottery center, cibiyar zata kasance kan gaba wajan jan hankalin masu son yawon bude ido a ciki da wajan kasan nan.

Ya kara da cewar cibiyar, ba nuna al’adu kadai ba, zata kuma kara farfado da harkokin yawon bude ido wanda ke zama mahimmi ga hanyoyin samar da kudaden shiga ga gwamnatin jihar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *