Take a fresh look at your lifestyle.

Farisa Ta Kera Babban Jirgi Mara Matuki Da Tara Labarai

0 132

Kasar Iran ta kera wani jirgin sama mara matuki na gida mai suna Mohajer-10 tare da ingantacciyar tazara da tsawon lokaci tare da daukar nauyi mai yawa, in ji kafar yada labaran kasar Farisa.

 

Kafafen yada labarai sun ce jirgin maras matuki yana da tafiyar kilomita 2,000 (mil 1,240) kuma yana iya tashi har zuwa sa’o’i 24, nauyinsa zai iya kai kilogiram 300 , wanda ya ninka karfin jirgin “Mohajer-6”.

 

Bidiyon da kafafen yada labarai na Farisa suka fitar ya nuna jirgin mara matuki a tsakanin sauran kayan aikin soja, tare da rubutu yana cewa “shirya matsugunin ku” a cikin Ibrananci da Farisa.

 

An buga shi a ranar masana’antar soja ta Farisa, rubutun faifan bidiyon yana nuna tashin hankali tsakanin manyan abokan gaba Farisa da Isra’ila.

 

 

 

REUTERS   Ladan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *