Kotu Ta Wanke Tsohon Firayim Ministan Pakistan Khan daga tuhumar kisan kai – Lauya
Maimuna Kassim TukurAbuja Maimuna Kassim TukurAbuja
A ranar Litinin ne wata kotu a Pakistan ta yi watsi da zargin kisan kai da ake yi wa tsohon Firaminista Imran Khan, in ji lauyansa.
“Allah yabamu albarka,” in ji lauyan, Naeem Panjutha a dandalin aika sako na X, wanda akafi sani da Twitter, ya kara da cewa wata kotu ta kori tuhumar da ake yi da kisan wani lauya a Kudancin birnin Quetta.
Khan, wanda aka tuhume shi da kisan kai a watan Yuni, yana fuskantar shari’o’i sama da 100 tun bayan hambarar da shi a kuri’ar amincewa da majalisar dokokin kasar a watan Afrilu, 2022, bayan da ya yi karo da sojojin kasar.
Wata babbar kotu a Islamabad ita ma a yau litinin za ta yanke hukunci kan karar da Khan ya shigar na neman a dakatar da hukuncin da aka yanke masa kan wata shari’a da ake zarginsa da aikatawa.
REUTERS
Maimuna Kassim Tukur.
Leave a Reply