Firayim Ministan Indiya Ya Bada Shawarar Na Shigar Da Tarayyar Afirka Cikin Kungiyar G20

Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta zama memba a kungiyar G20, kungiyar kasashe mafi arziki a duniya da za ta hadu a Indiya a watan Satumba.
Narendra Modi ya ce, “Mun gayyaci kungiyar Tarayyar Afirka tare da ra’ayin ba ta matsayin memba na dindindin” na G20, in ji Narendra Modi yayin taron kasuwanci na B20 wanda aka gudanar gabanin taron G20 a ranakun 9 da 10 ga Satumba.
A watan Disamba, shugaban Amurka Joe Biden ya riga ya bayyana fatan kungiyar Tarayyar Afirka ta shiga G20 a matsayin mamba na dindindin, yana mai tabbatar da cewa “hakan zai faru”.
Ƙasar Afirka ɗaya ce kawai, Afirka ta Kudu, a halin yanzu mamba ce ta G20, wacce ta haɗa 19 daga cikin manyan ƙasashe masu karfin tattalin arziki na duniya da Tarayyar Turai, wanda ke wakiltar 85% na GDP na duniya da kashi biyu bisa uku na al’ummar duniya.
Kungiyar AU tana da hedkwata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, tana da kasashe 55 membobi, adadin da ya kai dala tiriliyan uku a cikin GDP.
Firayim Ministan Indiya ya kuma tabbatar da cewa kasarsa, babbar abokiyar hamayyar kasar Sin, tana da karfin rama matsalolin wadatar kayayyaki da rikicin Covid ya haifar.
Indiya ita ce “mafita” don ƙirƙirar ” sarkar samar da kayayyaki ta duniya abin dogaro “, saboda “duniya ta canza da yawa bayan Covid-19”, in ji Mista Modi.
A ranar Alhamis a gun taron kolin BRICS (rukunin manyan kasashe masu tasowa) a Afirka ta Kudu, Mr Modi ya tattauna kai tsaye da shugaban kasar Sin Xi Jinping.
Africanews/Ladan Nasidi.
Leave a Reply