Take a fresh look at your lifestyle.

SA ta taya shugaban kasar Zimbabwe murna yayin da wasu ke sukar zaben

4 146

Kasashen Afirka ta Kudu da Rasha da China sun taya shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa murnar lashe zaben da aka gudanar a karshen mako.

 

A halin da ake ciki, Amurka ta kara da muryarta ga karuwar sukar babban zaben da aka yi a makon da ya gabata wanda ‘yan adawa suka bayyana a matsayin “magudi”.

 

Gwamnatin Amurka ta ce ana nuna kyama ga ‘yan adawa tare da bayyana sahihan rahotanni da ke cewa an tilasta wa masu sa ido sauya wasu fom na sakamakon zabe. Hukumar zaben ta yi watsi da wadannan ikirari.

 

Sanarwar da fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta fitar ta ce, Afirka ta Kudu na sane da cewa an gudanar da zaben ne a cikin mawuyacin hali na tattalin arziki saboda takunkumin da aka kakaba wa Zimbabwe.

 

Ta kuma amince da damuwar da masu sa ido kan zabukan masu zaman kansu suka nuna game da sahihancin sakamakon.

 

Wasu masu sa ido sun ce zaben ya gaza cika ka’idojin kasa da kasa da kuma bukatun kundin tsarin mulkin Zimbabwe.

 

Kasashen Afirka ta Kudu, Rasha da China, su ne manyan abokan cinikayyar kasar Zimbabwe, kuma goyon bayansu ga zaben na da matukar muhimmanci, yayin da Zimbabwe ke fuskantar yiwuwar kara warewa kasashen yammacin duniya takunkumi, bayan sukar da aka yi wa zaben.

 

Jam’iyyar adawa ta Citizens Coalition for Change na ci gaba da tattara nata sakamakon kafin ta yanke shawarar wani sahihin shiri na abin da zai yi na gaba. Sai dai sakon taya murna ga shugaba Mnangagwa wata kila nuni ne da cewa manyan aminan kasar Zimbabwe a shirye suke su ci gaba da karbar sakamakon zaben.

 

BBC/Ladan Nasidi.

4 responses to “SA ta taya shugaban kasar Zimbabwe murna yayin da wasu ke sukar zaben”

  1. Please let me know if you’re looking for a writer for your
    blog. You have some really great articles and I feel I would be a good asset.
    If you ever want to take some of the load off, I’d love to write some content for your blog
    in exchange for a link back to mine. Please shoot me an e-mail if interested.

    Thank you!

  2. Quer começar a apostar com um impulso extra? Na monicafepc962398.blognody.net, novos usuários recebem um bônus de 100 dólares assim que finalizam o
    cadastro. Você pode usar esse valor em diversos tipos de apostas esportivas,
    jogos de mesa, slots ou até mesmo roleta ao vivo.

    Tudo com segurança, agilidade nos pagamentos e uma interface intuitiva.
    A promoção é válida por tempo limitado, então
    não perca tempo. Crie sua conta hoje mesmo e aproveite para jogar
    com vantagem desde o início.

  3. Wow! After all I got a website from where I know how to
    genuinely get helpful information regarding my
    study and knowledge.

  4. hello!,I really like your writing very a
    lot! proportion we keep in touch more about your post on AOL?

    I require a specialist on this house to resolve my problem.

    Maybe that is you! Having a look forward to look you.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *