Majalisar dokokin jihar Filato ta kara yawan kwamitoci 19 na majalisar, wanda adadin ya kai 24.
Shugaban majalisar, Moses Sule, ya bayyana kundin tsarin mulkin karin kwamitocin yayin zamanta na ranar Talata.
Da yake bayyana kwamitocin, shugaban majalisar ya umurci magatakardar majalisar da ya shirya jerin sunayen wadanda za su yi aiki a matsayin sakatarorin kwamitoci tare da mika wa ofishinsa.
Shugaban majalisar ya yi gargadin cewa kada a nada darakta don zama sakataren ko wane kwamiti ya kara da cewa babu wani kwamiti da zai fara aikin sa ido ba tare da amincewar shugaban majalisar ba.
A cewar kakakin, kwamitin ilimi, kimiyya da fasaha zai kasance karkashin jagorancin Mista Philip Jwe tare da Mista Nanbol Rimvyat a matsayin mataimakiyar shugaba, Misis Salome Wanglek ita ce za ta jagoranci kwamitin lafiya tare da Mista Cornelius Doeyok a matsayin mataimakin shugaba.
Shugaban majalisar zai jagoranci kwamitin kula da asusun yayin da mataimakinsa Gwottson Fom, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.
Maimuna Kassim Tukur.
Leave a Reply