Take a fresh look at your lifestyle.

Tsohon Shugaban Gabon Na Tsare A Daurin Talala – Sojoji

0 203

Wasu gungun hafsoshin soja a kasar Gabon da ke tsakiyar Afirka sun ce sun tsige shugaba Ali Bongo daga mukamin shi tare da yima shi Daurin Talala.

 

Jami’an sun sanar da juyin mulkin da safiyar Laraba a gidan talabijin na kasar Gabon 24, ‘yan kwanaki kadan bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da cewa Bongo ya sake lashe zabe karo na uku a babban zaben kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

 

Jami’an sun ce sakamakon zaben ya lalace, an kuma ruguza dukkanin cibiyoyin gwamnati, an kuma rufe dukkan iyakokin kasar har sai an ba da sanarwar.

 

“Mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen mulkin da ake yi a yanzu,” in ji daya daga cikin jami’an.

 

Sa’o’i kadan bayan sanarwar farko, jami’an sun sake fitar da wani faifan bidiyo suna ikirarin cewa sun tsare Bongo.

 

A shekara ta 2009 ne Bongo ya fara mulki, bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo wanda ya zama shugaban kasar mai arzikin man fetur a shekarar 1967.

 

Zaben na ranar Asabar ya cika da rashin masu sa ido na kasa da kasa, lamarin da ya kara nuna damuwa kan gaskiya.

 

Bayan haka gwamnatin Bongo ta takaita ayyukan intanet tare da sanya dokar hana fita na dare a duk fadin kasar, tana mai cewa ya zama dole a hana yada labaran karya.

 

Da alama an sake dawo da hanyoyin shiga Intanet aƙalla bayan sanarwar juyin mulkin.

 

 

An ji karar harbe-harbe a ko’ina cikin babban birnin kasar Gabon, Libreville, bayan fitowar da jami’an suka yi a gidan talabijin na farko.

 

Mazauna yankin daga baya sun yi ta kwarara kan titunan Libreville domin murnar labarin tsige Bongo.

 

Juyin mulkin da aka ayyana ya zo ne a daidai lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Nijar a watan da ya gabata, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin juyin mulkin da aka yi a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka tun shekara ta 2020.

 

Shugaba Bongo ya tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Janairun 2019 a lokacin da yake murmurewa daga bugun jini.

 

 

VOA/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *