Wata gidauniyar mai ba da tallafi ga wadanda matsalar tsaro ta shafa wato Victims Support Fund (VSF) a Turance, hadin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina da ke Arewa maso ‘yammacin Najeriya ta kaddamar da rabon kayan masarufi ga wadanda matsalar tsaro ta shafa kuma ta rabo su da muhallan su a kananan hukumomi uku da ke jihar
‘Yan gudun hijirar wadanda suka amfana da tallafin kayan masufi da suka hada da buhunan shinkafa da wake da man girki an zabo su ne daga kananan hukumomin Batsari da Jibia da karamar hukumar Faskari a shiyyar Funtua da ke jihar
Sauran kayayyakin da’yan gudun hijirar suka amfana da su sun hada da jakar magi da suga da gishiri da dai sauran kayan masarufi domin rage masu radadin abin da ya same su
Da take ganawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da rabon kayan a birnin Katsina, Babbar daraktar gidauniyar ta VSF, Farfesa Nana Tanko ta bayyana cewa wadanda suka amfana an zabo su ne a tsanake daga cikin wadanda lamarin ya shafa kuma suka kasance mafi bukatar tallafin a yankunan da lamarin ya faru
Babbar daraktar ta ce daga cikin wadanda aka tallafa mawa akwai Iyaye mata dubu biyu da dari hudu da arba’in da hudu (2,444) da kuma magidanta maza dubu daya da dari biyar da hamsin da shidda (1,556)
Tayi nuni da cewa an kafa gidauniyar ne a shekarar 2014 domin tallafa ma magidanta a jihohi guda tara (9) da matsalar tsaro ta shafa a Najeriya
Farfesa Tanko ta jaddada kudurin gidauniyar wajen tabbatar da tallafin ya isa ga dukkanin jihohi da yankuna da matsalar tsaron ta shafa domin rage radadi ga wadanda lamarin ya shafa.
A nasa jawabin a wajen taron, mataimakin gwamnan jihar Katsina wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan sa, Mukhtar Saulawa ya godema Gen.T.Y. Danjuma, shugaba kuma wanda ya kafa gidauniyar ta VSF bisa tallafa ma wadanda lamarin ya shafa a jihar Katsina, yana mai bada tabbacin gwamnatin jihar na yin dukkanin abinda ya kamata domin tallafin ya isa ga wadanda suka cancanta.
Kamilu Lawal Katsina
Leave a Reply