Take a fresh look at your lifestyle.

Kudaden Shiga FCT za’a Aiwatar Da Wasu Ayyuka- Ministan

0 144

Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, FCT, Nyesom Wike, ya sanar da cewa, a gaba, za a danganta kudaden shiga na cikin gida (IGR) na Abuja, babban birnin kasar da aiwatar da wasu ayyuka na musamman.

 

Ministan, a yayin da yake magana kan wasu batutuwa masu muhimmanci da ke bukatar daukar kwararan matakai don gyara munanan al’amura a Abuja, ya bayyana cewa, yin hakan zai taimaka wajen aiwatar da wasu tsare-tsare a kan lokaci ba tare da dogaro da kasafin kudi kawai ba.

 

Don haka ya ba da shawarar cewa duk wanda ya kaucewa biyan kudin hayar kasa da harajin da ake bin FCTA to ya gaggauta warware basussukan da ke kan su. Ya kuma jaddada cewa, ba tare da la’akari da matsayinsu na zaman jama’a ba, Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar mataki kan wadanda suka gaza wajen karbar abin da ya dace na FCTA.

 

Ministan babban birnin tarayya Abuja ya nuna damuwarsa kan yadda akasarin masu rike da mukamai ne ke da alhakin kawo cikas ga kokarin da gwamnatin babban birnin tarayya ta yi na maido da babban tsarin Abuja.

 

Ministan ya yi amfani da wannan dandali ne wajen yin ishara da kudaden da aka ware na naira miliyan 825 ga ‘yan asalin kasar da aka ware filayensu domin bunkasa titin jirgin sama na biyu na Abuja. Saboda haka, ya umurci Babban Sakatare da ya raba kudaden da aka ce kafin karshen mako don hanzarta tare da daidaita tsarin gina titin jirgin sama.

 

Wike ya ci gaba da bayyana cewa gwamnatinsa na fama da bashi (garnishee order) da ya kai dala miliyan dari takwas akan gwamnatin a gaban kotu, don haka akwai bukatar a binciko IGR domin samar da ayyuka, ganin yadda kasafin kudin kasa ke raguwa.

 

Da yake magana kan tasirin odar ga tattalin arzikin kasar, Ministan ya ce bashin ya isa ya samar da kasafin kudin FCTA na tsawon shekaru 10.

 

“Yaya zaki tsira? Su waye ke da alhakin wannan? Cewa babu ayyuka a cikin ƙasa, an yi watsi da komai. Akwai odar garnishee na $800m. Kun san abin da muke magana akai? Ta yaya za mu tsira? Ku je ku ga abin da ya faru. Garnishee oda nan da can.

 

“Wurin ya lalace kawai… Ta yaya za mu tsira da shi? To yanzu ka ce mun zo mu yi mu’ujizai, wace mu’ujiza? Ina zan samu kudin da zan je in biya $800m?” Wike yayi kuka.

 

 

Ladan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *