Gwamnatin Tarayyar Najeriya na jimamin rasuwar mai zanen tutar Najeriya, Pa Taiwo Akinkunmi wanda ya rasu yana da shekaru 84 a duniya, a gidan iyalansa dake Ibadan, bayan gajeruwar rashin lafiya.
“Na yi matukar bakin ciki da labarin rasuwar Pa Taiwo Akinkunmi, fitaccen dan kasar nan, wanda gudunmawarsa ga hadin kan kasa ba za ta gushe ba,” in ji ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Mohammed Idris a wata sanarwa da ya fitar a hukumance.
Ministan ya lura da rasuwar Pa Akinkunmi a lokacin da Najeriya ke sake farfado da kanta don samar da zaman lafiya, ci gaba da kuma dawwama a sulhunta kasa, ya kuma kara da cewa kasar zata rasa irin gudunmawar da marigayin zai bayar, musamman a wannan lokaci da gwamnati karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu take da tsarin Ajenda me taken Renewed Hope don ginawa a kan kishin kasa wanda ke nuna tafiyar Najeriya ta samun ‘yancin kai.
Ministan ya bayyana kwarin gwiwar cewa Pa Akinkunmi, wanda ake yi wa lakabi da Mista Tuta, zai ci gaba da rayuwa a cikin zukatan ‘yan Nijeriya har zuwa tsararraki masu zuwa.
Ya ce tutar kasa, daya daga cikin manyan tambarin Najeriya, za ta ci gaba da zama wata kadara wadda Pa Akinwunmi ya rubuta sunansa.
“Saboda haka, ina so in yi amfani da wannan damar wajen mika ta’aziyyata ga iyalansa, tare da addu’ar Allah ya ba su ikon jure wannan babban rashi.”
Leave a Reply