Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Juyin Mulki Ya Umarci ‘Yan Sanda Da Su Kori Jakadan Faransa

0 107

Gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta kwace mulki a watan da ya gabata ta ce ta kwace kariyar jakadan Faransa tare da umurtar ‘yan sanda da su kore shi.

 

Sylvain Itte visa da ta danginsa kuma an soke su.

 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai gwamnatin mulkin sojan kasar ta shaida masa cewa yana da sa’o’i 48 ya fice daga kasar a matsayin martani ga matakin da gwamnatin Faransa ta dauka wanda ta ce ya saba wa muradun Nijar.

 

Amma wa’adin ya wuce ranar Litinin ba tare da Paris ta kira shi ba.

 

Karanta kuma:

Juyin mulkin Nijar: Faransa ta ki amincewa da bukatar jakada ya bar Yamai

 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fada a ranar Litinin cewa jakadan zai ci gaba da zama a Nijar duk da matsin lamba daga gwamnatin soja.

 

Kuma ya jaddada goyon bayan Paris ga hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

 

Gwamnatin Faransa ta ce ba ta amince da jagororin juyin mulkin a matsayin halastattun shugabannin kasar ba.

 

Tun bayan hambarar da shugaban kasar, gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi amfani da kyamar Faransa a tsakanin al’ummar kasar don karfafa goyon bayanta.

 

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *