Take a fresh look at your lifestyle.

Kungiyar Kwadago Ta Jihar Neja Ta Bukaci Yin Adalci A Rabon Kayan Agaji

0 278

Kungiyoyin Kwadago a Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya, sun yanke shawarar karkatar da makudan kudade har naira miliyan 110, da aka ware tun farko a matsayin tallafin ga kungiyoyin masana’antu, domin amfanin ma’aikata da dama a jihar.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Neja, Kwamared Abdulkarim Idris Lafene ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Minna babban birnin jihar.

A cewar Lafene, “babban bukatar da ma’aikatan jihar Neja ke bukata shi ne biyan duk wani ma’aikaci da ma’aikata da masu ritaya a fadin gwamnatin jihar da kananan hukumomin jihar N50,000.

“Idiris Lafene ya ce “ana sa ran a rika saka wannan tallafin na kudi a cikin asusun albashi na ma’aikatan gwamnati da wadanda suka yi ritaya na tsawon watanni shida.”

Bugu da kari, shugaban kungiyar kwadago ta jihar ya bayar da umarni ga ma’aikata a jihar Neja, inda ya bukace su da su kaurace wa kwamitin da gwamnatin jihar Neja ta kafa na rabon kayan abinci, wanda aka shirya za a fara aiki gobe Laraba.

Kwamared Idris Lafene ya bayyana cewa da gangan gwamnati ta yi yunkurin cire ma’aikata da ‘yan fansho daga cikin ayyukan jin kai ya haifar da tashin hankali a tsakanin ’ya’yan kungiyoyin kwadago, wanda hakan ke haifar da kalubale ga ci gaban ma’aikata baki daya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *