Gwamnatin Katsina Ta Bukaci Masu Yima Kasa Hidima NYSC Su Tallafama Shirin Gwamnati
Kamilu Lawal Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta bukaci masu yiwa kasa hidima wato NYSC Corpers a turance da su jajirce wajen bada gudummuwsr su wajen cigaban al’umma a dukkanin yankunan da aka tura su domin aikin hidimar kasa na shekara guda
Kwamishinan ma’aikatar Matasa da Wasanni na jihar Katsina Yusuf Rabi’u Jirdede shine ya bukaci hakan a wajen rufe taron horar da matasan NYSC da aka turo jihar Katsina domin aikin bautar kasa a sansanin horar da matasan a birnin Katsina ranar Talata.
Jirdede wanda ya bayyana bukatar da ake da ita ga matasan da a ko da yaushe su kasance masu kokarin sauya al’amurra zuwa masu kyau, ya kuma bukace su da su kasance masu kishin hadin kai da zaman lafiyar al’umma da kasa baki daya
Yayi kira gare su da su isa dukkanin yankunan da aka tura su da kyakkyawar niyya, tare da jajircewa wajen bada gudummuwa ga al’ummomin da suka taras domin tabbatar da manufar shirin na hada kan al’umma da kuma cigaban kasa
Tun farko da take jawabi a wajen bikin rufe taron horaswar na mako ukku, Jami’ar hukumar NYSC a jihar Katsina Hajiya Aisha Muhammad ta bayyana cewa a tsawon mako Ukku da matasan su kayi a sansanin sun samu ilmi da kwarewa akan yadda zasu kasance a wuraren da aka tura su, tana mai kira garesu da su yi amfani da horan da suka samu tare da mutunta dabi’u da al’adun al’ummomin da suka samu Kansu a ciki
Ta kara da cewa an yi kyakkyawan tsari wajen tura matasan wuraren da ya kamata domin bada gudummuwa musamman a bangaren noma da cigaban karkara
Daga nan sai ta yabama gwamnatin jihar wajen tabbatar da samun nasarar horan da ayyukan hukumar ta NYSC a jihar ta Katsina
Kamilu Lawal Katsina
Leave a Reply