Take a fresh look at your lifestyle.

Japan Zata Karfafa Dangantaka Da Kudu Maso Gabashin Asiya- PM

0 113

Firayim Ministan Japan, Fumio Kishida ya fada a ranar Laraba cewa, Japan za ta karfafa goyon baya da hadin gwiwa tare da kasashen kudu maso gabashin Asiya a fannoni shida da suka hada da kayayyakin sufuri da na sintiri a teku.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron ASEAN-Indo-Pacific Forum (AIPF) a birnin Jakarta, wanda ke karbar bakuncin taron kungiyar kasashe ASEAN mai mambobi 10 na kasashen kudu maso gabashin Asiya a wannan mako.

 

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Sin ta tabbatar da kanta a cikin ruwan da ake takaddama a kai a yankin.

 

Kishida ya ce “Za mu bunkasa shirye-shiryen hadin gwiwa da dama a fannonin siyasa, tsaro, tattalin arziki, al’adu da zamantakewa.”

 

Kishida ya ce kasar Japan za ta ba da horo ga mutane 5,000 a cikin shekaru uku masu zuwa a fannoni shida, wadanda suka hada da hadin gwiwa kan harkokin yanar gizo.

 

Kishida ya kara da cewa, kasar Japan za ta kuma taimaka wajen kara karfin tabbatar da doka a teku ta hanyar horar da ma’aikata a hukumomin tsaron teku da ‘yan sandan ruwa, da kuma samar da jiragen ruwa na sintiri.

 

Biyo bayan barkewar cutar sankarau da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, Kishida ya kuma bayyana cewa Japan za ta karfafa sarkar samar da kayayyaki tare da yankin don tabbatar da daidaiton rarraba kayayyaki da amincin abinci.

 

 

 

REUTERS

Ladan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *