Akalla mutane 16 ne suka mutu sakamakon harin makami mai linzami da aka kai a birnin Kostyantynivka na kasar Ukraine.
Shugaban kasar Volodymyr Zelensky, wanda ya zargi Rasha, ya ce wadanda aka kashe “mutanen da ba su yi wani laifi ba” kuma ya yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.
Kostyantynivka, a yankin gabashin Donetsk na Ukraine, yana kusa da layin gaba.
Zelensky ya kara da cewa “Dole ne a ci nasara a kan wannan muguwar Rasha da wuri-wuri.”
Hukumomi a Masko ba su ce uffan ba game da ikirarin.
Daga cikin mutane 16 da suka mutu har da wani yaro, yayin da ake tunanin akalla wasu 20 sun jikkata, a cewar bayanin da Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya rabawa manema labarai.
“Dukkan ayyuka suna aiki,” in ji shi, ya kara da cewa “Gobarar tana dauke.”
An ba da rahoton an kai hari wata kasuwa, shaguna da wani kantin magani.
Har yanzu jami’ai a Rasha ba su dau alhakin kai harin ba. A baya dai sun musanta kai wa ‘yan kasar hari a wani bangare na harin da suke kai.
Harin na ranar Laraba ya zo daidai da ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai Kyiv babban birnin Ukraine, inda zai gana da Zelensky.
Kostyantynivka, wani ƙaramin gari na kasuwa, yana zaune kusa da fagen fama. Har ila yau yana da nisan mil 17 (kilomita 27) daga birnin Bakhmut, inda aka san cewa an dade ana gwabza fada.
BBC
LadanNasidi
Leave a Reply