Kungiya Ta Bukaci Gwamnati Ta Dauki Karin Malamai Don Koyar da Darasin Addini.
By Nura Mohammed, Minna
Kungiyar Kiristoci ta Kasa a Najeriya, CAN reshen Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta bukaci Gwamnati Jihar Neja da ta taimaka don daukan malamai da zasu koyar da darasin addini Krista na CRK a makarantun gwamnatin.
Shugaban Kungiyar Kiristocin a Jihar Neja, Rev. Dr. Bulus Damuwa Yahanna shine ya bukaci hakan a wajan Taron koli na Shugabannin kungiyar CAN na NACREN karo na 45 da ya gudana a Minna Fadar Gwamnatin Jihar Neja.
Rev. Dr. Bulus Damuwa Yahanna ya ce ” koyar da darasin zai taimaka wajan koyar da tarbiya da sanin kimar alumma musamman ga mabiya adinin.”
Shugaban ya Kara da cewar an Dan sami koma baya wajan samun kwararrun Malamai da ke koyar da darasin Wanda hakan ya Sanya mafi yawanci daliban da suka kammala karatun su Basa iya fahimtar irin mahimmancin dake tattare da koyarwar addini Krista.
“Darasin na taimakawa wajan fahimtar da dalibai da Kuma koyar da su ka’idoji da dokokin adinin domin zama alumma ta gari.” Rev. Dr. Bulus Damuwa Yahanna.
Tun da farko a jawabin sa Shugaban kungiyar NACREN ta kasa Rev. Dr. Reuben Maiture ya bukaci gwamnatin taraya da ta baiwa darasin mahimmanci domin a sami nasarar koyar da alumma dabi’a ta gari.
Ya Kara da cewar rashin isasaun malaman ne ta Sanya kungiyar Neman malaman Sakai don koyar da darasin kyauta.
Leave a Reply