Take a fresh look at your lifestyle.

Rasha Ta Kai Harin Makami Mai Linzami Akan A Ginin ‘Yan Sandan Ukraine- Ministan Harkokin Cikin Gida

0 138

Wani makami mai linzami na Rasha ya harba wani ginin ‘yan sanda a birnin Kryvyi Rih da ke tsakiyar kasar Ukraine a ranar Juma’a, inda ya kashe dan sanda tare da jikkata wasu da dama, in ji ministan harkokin cikin gida Ihor Klymenko.

 

 

An lalata ginin hukumar ‘yan sanda tare da fitar da mutane da dama daga cikin baraguzan ginin bayan harin da aka kai a mahaifar shugaban kasar Volodymyr Zelenskiy, in ji Klymenko a cikin manhajar aika sakon Telegram.

 

 

Ya sanya adadin wadanda suka jikkata  25. Kana mutane 40 suka ji raunuka.

 

 

“An kashe wani dan sanda sakamakon harin da Rasha ta kai,” in ji Klymenko.

 

 

Gwamnan yankin Serhiy Lysak ya ce gine-ginen gudanarwa guda uku sun lalace, kuma an bata wasu gine-gine bakwai da suka hada da wani katafaren gini.

 

 

Har ila yau Rasha ta kai hari da jiragen yaki mara matuki karo na biyar a cikin wannan mako a yankin kudancin Odesa dake da tashar jiragen ruwa na Ukraine a tekun Black Sea da kuma kogin Danube wadanda ake amfani da su wajen fitar da hatsi da sauran kayayyakin amfanin gona.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *