Take a fresh look at your lifestyle.

Mutum Daya Ya Mutu Bayan Da Jirgin Helikwafta Ya Fado A Tekun Dubai

0 161

Matukin jirgi daya ya mutu a lokacin da wani jirgin sama mai saukar ungulu na AeroGulf ya fado cikin teku kuma ana ci gaba da neman wani matukin jirgin, in ji Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

 

 

Hadarin ya afku ne a gabar tekun Dubai bayan da jirgin mai saukar ungulu ya tashi daga filin jirgin saman Al Maktoum. Daya daga cikin matukan jirgin mai saukar ungulu kirar Bell 212 dan kasar Masar ne, dayan kuma dan kasar Afirka ta Kudu ne, in ji hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama.

 

 

“Har yanzu ana ci gaba da neman matukin jirgin da ya bace,” in ji hukumar.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *