Ministan Harkokin Wajen Japan Zai Gana Da Takwaran Shi Na Ukraine
Ministan harkokin wajen Japan Yoshimasa Hayashi zai gana da takwaran shi na Ukraine Dmytro Kuleba a birnin Kyiv, in ji ma’aikatar harkokin wajen Japan.
A tattaunawarsa da Kuleba, Hayashi zai jaddada goyon bayan kasar Japan ga Ukraine tare da yin jawabi kan shigar da kasashen duniya ke yi don kawo karshen mamayar da Rasha ke yi a Ukraine cikin gaggawa, in ji ma’aikatar cikin wata sanarwa.
Hayashi yana tare da shugabannin kamfanonin Japan, ciki har da Hiroshi Mikitani, wanda ya kafa kuma babban jami’in Rakuten Group, in ji ma’aikatar.
Rahoton ya ce Firayim Ministan Japan Fumio Kishida ya kai ziyarar ba-zata a Kyiv domin ganawa da shugaban Ukraine Volodomyr Zelenskiy a watan Maris.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply