Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Umar Bago Ya Bukaci Yan Jihar Su Shiga Cikin Shirin Gwamnati Na Gina Sabuwar Jihar Neja

By Nura Mohammed, Minna

0 221

Gwamnan Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya, Umar Mohammed Bago ya bukaci alummar jihar da su shiga cikin shirin kara gina sabuwar jihar Neja da gwamnatin ta tsara domin bada tasu gudumuwa.

Gwamnan ya bukaci hakan ne a wajan taron karrama yan jihar dake rike da mukaman siyasa zababbu da kuma wadanda aka nada, a dakin taro na Justice Idiris Legbo Kutigi dake Minna fadar gwamnatin jihar.

A cewar sa babban makasudin shirya wannan taron shine don hada kan masu ruwa da tsaki domin samar da sabuwar jihar Neja. “Taron zai samar da daidaito ta hanyar tattauna matsalolin jihar domin ciyar da ita gaba, inda kuma za a Rlrika yin taron a duk bayan watanni hudu, a don haka nake sun suma dukkanin kananana hukumomi 25 su samar da irin hakan a yankunansu”

Gwamnan ya kuma bukaci ministocin biyu da suka fito daga jihar, ministan sadarwa da wayar da kan alumma na kasa Mohammed Idiris Malagi da karamin ministan albarkatun noma da samar da abinci, Aliyu Abdullahi Sabi da su yi anfani da mukaman su wajan ciyar da jihar gaba. Inda ya ce jihar nada fadin kasa ya bukaci ministan da ya sanya jihar a cikin tsare tsaren gwamnatin taraya na farfado da harkokin noma a fadin kasar.

A yayin taron, dukkanin ministocin biyu sun Yaba da irin tsarin da gwamna Umar Mohammed Bago yake shirin dauka, wanda hakan zai kawo hadin Kai a tsakankanin su ta yadda za a kai ga samar da sabuwar jihar Neja.

A jawaban su daban daban a taron, sanata Mai waliktan kudancin jihar Neja Sanata Peter Jiya Ndalikali da kakakin majalisar dokokin jihar Abdulmalik Sarkin Daji da wakilin Shugaban majalisar sarakunan jihar Sarkin Bidda Alhaji Yahaya Abubakar, Mai martaba Sarkin kontagora Alhaji Muhammad Barau sun sha alwashin bada hadin kai don ganin an sami nasarar tafiyar.

Gwamnatin Jihar Neja ne ta shirya taron karrama yan jihar dake rike da mukaman siyasa, kama daga ministoci da sanatoci da Yan majalisun taraya dake wakiltan jihar da yan majalisun dokokin jihar da kwamishinonin da Kuma manyan masu baiwa Gwamnan shawarwari wato special Advisers, domin hada kan su don ganin an yi aiki tare wajan ciyar da jihar gaba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *