Take a fresh look at your lifestyle.

Jam’iyyar Putin Ta Lashe Kuri’u A Yankunan Ukraine Da Ta Mamaye

0 143

Kasar Rasha ta kammala zabukan yankuna da na kananan hukumomi da aka yi watsi da su, da suka hada da na yankuna hudu na Gabashin kasar da aka kwace daga Ukraine, inda suka bayar da gagarumin goyon baya ga shugaba Vladimir Putin.

 

 

Zaben da aka kwashe mako guda ana yi a ranar Lahadin da ta gabata, ya gudana ne a daidai lokacin da ake sukar magudin zabe da kuma yunkurin Ukraine na kwato yankunanta.

 

 

Majalisar Turai, babbar kungiyar kare hakkin Turai, ta kira zaben a matsayin cin zarafi ga dokokin kasa da kasa, yayin da Kyiv da kawayenta suka ce wani yunkuri ne da ba bisa ka’ida ba na kara matsawa Moscow karfi a yankuna a Kudu da Gabashin Ukraine.

 

 

Bayanan da Moscow da jami’an wakilai suka wallafa sun nuna cewa masu kada kuri’a a yankunan Donetsk da Luhansk da Zaporizhia da Kherson da ke fama da yakin Ukraine sun goyi bayan jam’iyyar Putin ta United Russia da fiye da kashi 70 cikin 100 na kuri’un da aka kada a kowane yanki, in ji kamfanin dillancin labarai na gwamnati.

 

 

Ba a fitar da cikakkun alkaluma na zaben ba.

 

 

Sai dai kawai ‘yan kawayen Rasha sun amince da yankunan a matsayin wani bangare na Ukraine.

 

 

Sakamakon ya nuna cewa Gwamnonin da aka zabo na Moscow a yankunan, da suka hada da tsofaffin shugabannin ‘yan aware da kuma kananan ‘yan siyasa na cikin gida masu goyon bayan Rasha, sun samu cikakken wa’adin mulki.

 

 

Babu ɗayan yankuna huɗu da sojojin Rasha ke da cikakken iko.

 

 

Ukraine, wacce a watan Yuni ta fara wani mummunan farmaki na ‘yantar da filayen, sannu a hankali ta sake dawo da yankuna a yankin Zaporizhia kuma ta yi ikirarin wasu ci gaba a Donetsk a kusa da birnin Bakhmut da ya rushe.

 

 

 

ALJAZEERA/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *