Take a fresh look at your lifestyle.

NITDA Ta Gina Cibiyar Tattalin Arzikin Dijital A Kudancin Kaduna

0 182

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) ta samu kayayyakin da za a girka a garin Kafanchan da ke Jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya, domin saukaka ayyukan na’urorin zamani.

Wannan ya biyo bayan amincewar tura Cibiyar Tattalin Arziki ta Dijital (DEC) a yankin.

Shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kafanchan (Senior), Mista Simon Yusuf ya karbi kayan aikin ne domin ganin an kaddamar da cibiyar horar da mata da matasa 300 cikin sauki a makarantar.

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) ce ta bayar da tallafin kayan aikin bayan amincewa da aikin da Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa ta kasa ta 10 ya yi.

Da yake karbar kayan aikin a harabar makarantar da ke garin Kafanchan, Shugaban makarantar, ya gode wa Sanatan da ya zabo makarantar domin gudanar da wannan aiki, inda ya yi alkawarin za su jajirce wajen kiyaye kayayyakin domin amfanin kowa da kowa musamman dalibai.

Daga cikin dukkan kayayyakin da ake sa ran za a tashi daga cibiyar ba tare da wata matsala ba, shugaban makarantar ya tabbatar wa manema labarai cewa ya karbi sama da kashi 80 cikin 100 na su.

A cikin gaggawar mayar da martani ga ci gaban, dan majalisar ya yaba wa NITDA saboda saurin tura kayan aikin ICT tare da lura da cewa, zai fassara zuwa ga al’umma mai wayewa ta dijital.

Idan aka kammala, Cibiyar Tattalin Arziki ta Dijital za ta kasance tana da kwamfutoci, haɗin Intanet, cibiyar sadarwa ta gida (LAN), hanyar ilmantarwa ta e-learning, inverter mai amfani da hasken rana, janareta, da sauransu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *