Gwamnan Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Umar Mohammed Bago, ya ce Gwamnatin sa zata yi gyaran hanyoyi da kuma yin wasu sabbin hanyoyi da suka kai tsawon kilomita 1,500 cikin shekaru 4 masu zuwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajan kaddamar da sabbin ayyukan da kuma gyran tsoffin hanyoyi a Minna fadar Gwamnatin Jihar.
Gwamna Umar Mohammed Bago ya kara da cewar za a Yi sabuwar hanya mai tsawon kilomita 202 a birnin Minna wanda hakan zai kawo cigaba ga birnin.
Gwamna Bago ya ce “gwamnatin jihar Neja Zata Yi duk abun da ya kamata wajan gudanar da ayyukan cigaba ga alummar jihar Neja batare da duba ko aikin na gwamnatin taraya ne ba, bayan kammala ayyukan gwamnatin jihar zata zata nemi hakkokinta ga gwamnatin taraya.”
Har ila yau gwamna Umar Muhammad Bago ya ce aikin zai kuma samar da karin ayyukan Yi ga dinbin matasan jihar, da kuma karawa masu kananana sana’oi karfi.
Da yake jawabi tun da farko, kwamishinan ayyuka Sulaiman Umar ya ce an raba ayyukan ne zuwa gida biyu, inda a zangon farko za a Yi aikin hanyar kilomita 202 da suka kunshi manyan hanyoyi 22.
Inda kashin farko ya kunshi hanyoyi 8 yayin da kashi na biyu ya kunshi hanyoyi 14 da suka hada da gadar sama.
Kwamishinan ya Kuma Kara da cewar za a kuma kammala ayyukan cikin sauri kamar yadda kamfanin ya shedawa gwamnati.
Shugaban kamfanin na CCECC da aka damkawa aikin Mr David Wang ya yabawa Gwamnan bisa tunanin sa na kwawata jihar Neja, ta bijiro da ayyukan hanyoyi domin Kai jihar gaba ta fanin cigaba.
A jawabin sa a Taron Mai martaba Sarkin Minna Umar Faruq Bahago ya yabawa Gwamna Umar Mohammed Bago, inda ya ce Gwamnan ya nuna da gaske yake wajan ciyar da jihar Neja gaba.
Bayan kammala aikin hanyoyin, ana saran samun Karin kadada 100 na tsawon titunan Wanda hakan zai kawowa jihar karin cigaba a fafotukar da Gwamnan ke Yi na Nemo masu son zuba jari a jihar.
Leave a Reply