Rundunar Sojin Ukraine ta fada jiya Juma’a cewa dakarunta sun kwace wani kauye kusa da Bakhmut, birnin Gabashin da ya fada hannun Rasha a watan Mayu bayan da aka yi masa kawanya tsawon watanni.
Bangaren Rasha ya yi hasarar rayuka da asarar kayayyakin aiki, yayin da sojojin Ukraine suka yi nasarar karfafa wasu yankuna, in ji babban hafsan sojin Ukraine a wani rahoton safiya.
“A yayin farmakin da suka kai, sun kama Andriivka a yankin Donetsk,” in ji Babban Jami’in.
Kauyen Andriivka yana kudancin Bakhmut, wurin da aka gwabza kazamin fada tun bayan mamayar da Rasha ta yi a watan Fabrairun bara.
Babban Hafsan Hafsoshin ya kuma bayar da rahoton “nasara ta wani bangare” kusa da kauyen Klishchiivka, kudu da Bakhmut.
A cikin watanni uku da ta kwashe watanni uku ana gwabzawa, Ukraine ta ba da rahoton jinkiri,da ci gaba da aka samu a kan matsayi na Rasha, ta sake kwace wasu kauyuka tare da ci gaba a gefen Bakhmut.
Shugaban kasar Volodymyr Zelenskiy da wasu jami’ai sun yi watsi da masu sukar kasashen yammacin duniya wadanda suka ce harin ya yi tsauri da kura-kurai.
A bangaren kudancin kasar kuwa, Janar din ya ce dakarun shi na yin asara mai yawa kan abokan gaba da ke kusa da kauyen Verbove da ke yankin Zaporizhzhia.
REUTERS/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply