Take a fresh look at your lifestyle.

Zanga-zangar da aka yi a Indonesiya Ta Yi Sana diyar Korar dubban mutane daga birnin ‘Eco-City’

0 105

Zanga-zangar ta afku a lardin Riau na kasar Indonesiya yayin da mazauna tsibirin Rempang suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da shirin gwamnati na korar dubban mutane domin samar da wata masana’antar gilashin biliyoyin daloli mallakar kasar Sin da kuma ‘Eco-City’.

 

kan korar Rikicin ya dau tsawon watanni, bayan da gwamnati ta sanar da cewa mazauna Rempang 7,500 za su ƙaura zuwa cikin ƙasa, kimanin kilomita 60 (mil 37) daga gidajensu na bakin teku. Mutane da yawa suna rayuwa daga teku, suna sayar da kifi da aka kama a cikin gida, kaguwa,da sauran kayan abinci daga teku.

 

Sai dai a yanzu da aka sanar da mazauna yankin cewa sai a karshen wannan watan su fice kuma zanga-zangar ta kara kamari.

 

A cikin ‘yan kwanakin nan, masu zanga-zangar sun fuskanci ‘yan sanda da sojoji a wurare da dama a Riau, ciki har da Rempang da Batam, birni mafi girma a cikin tsibirin, wanda ke kudu da Singapore.

 

Ana zargin ‘yan sandan da suka yi amfani da karfin tuwo da hayakin Barkonon tsohuwa kuma an kama mutane da dama.

 

Yayin da shirye-shiryen bunkasa Rempang ke cikin ayyukan kusan shekaru 20, mazauna yankin sun ce a farkon watan Satumba ne aka sanar da su cewa za su fita daga kauyukansu kafin karshen wata.

 

Sanarwar ba zato ba tsammani ta girgiza mazauna da yawa tare da sake haifar da sabon zanga-zanga, ciki har da taron makon da ya gabata a Rempang.

 

 

Da yake magana a fadar shugaban kasa, Ministan Harkokin Siyasa, Shari’a, da Tsaro Mahfud MD ya ce lamarin yana bukatar “a kula sosai”.

 

 

 

ALJAZEERA/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *