Gidauniyar CLEEN Ta Yi Taron Wayar Da Kan Jama’a Don Tabbatar Da Adalci Ga Masu Aikata Laifuka
Hadiza Halliru, Sokoto
Gidauniyar CLEEN foundation mai zaman kanta tare da hadin gwiwar Mac-Arthur sun gudanar da taron karawa juna sani na kwana biyu domin wayar da kan masu ruwa da tsaki domin ganin an tabbatar da adalci a tsakanin masu aikata laifuka a Najeriya.
An tsara dokar ne domin maido da adalci da kare mutuncin kowane dan kasa, sannan an tabbatar da cewa babu wata kasa da za ta ci gaba idan ba a kare mutuncin al’ummarta ba.
Mista Salawudeen Hashim darekta ne a cibiyar CLEEN foundation ya bukaci masu ruwa da tsaki da su bada cikakken goyon baya ta hanyar wayar da kan al’umma tare da bada rahotanni domin dokar ACJA/ACJL ta kasance mai muhimmanci ga kowane dan kasa.
Ga rahoton Hadiza Haliru Muhammad daga Sakkwato:
Abdulkarim Rabiu