Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Nada Cardoso A Matsayin Sabon Gwamnan CBN

0 339

 

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dr. Olayemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), na tsawon shekaru biyar (5) a matakin farko, har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da shi.

 

Sanarwar hakan ta fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale.

 

Ya ce; “ Umarnin ya yi daidai da sashe na 8 (1) na dokar babban bankin Najeriya na shekarar 2007, wanda ya baiwa shugaban tarayyar Najeriya ikon nada gwamna da mataimakan gwamnoni hudu (4) a babban bankin Najeriya. (CBN), har sai majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta tabbatar da hakan.”

 

Bugu da kari, shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin sabbin mataimakan gwamnonin babban bankin Najeriya; Mrs. Emem Usoro, Muhammad Abdullahi Dattijo, Mista Philip Ikeazor, da Dr. Bala Bello.

Sabbin Mataimakan Gwamnoni hudu da aka amince da su, za su yi aiki na tsawon shekaru biyar (5) a matakin farko, har sai Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da su, kamar yadda ta lissafo a kasa:

 

“A bisa tsarin sabunta bege na Shugaba Bola Tinubu, shugaban na fatan wadanda aka zaba a sama za su samu nasarar aiwatar da muhimman sauye-sauye a babban bankin Najeriya, wanda zai kara kwarin gwiwar ‘yan Najeriya da abokan huldar kasa da kasa wajen sake fasalin tattalin arzikin Najeriya wajen dorewa. ci gaba da wadata ga kowa da kowa,” sanarwar ta kara da cewa.

 

 

Ladan Nasidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *