Kungiyar Friday For Future (FFF) , ta yi kira da a kawo karshen anfani da nau’ingawayi da idkar Gas a Najeriya.
Mista Kingsley Odogwu, kodinetan kungiyar na kasa kuma wakilin kungiyar ne ya bayyana haka a taron yakin neman zabe na tattakin adali ga yanayi, ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce wannan gangamin an yi shi ne da nufin wayar da kan jama’a kan illolin da hayaki daga gawayi ke haifarwa da kuma bukatar gwamnatin tarayya ta neo hanyoyin samar da makamashi.
Ya ce yayin da shugabannin kasashen duniya ke taruwa a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin New York a watan Satumba, ya zama wajibi Najeriya ita ma ta yi na’am da bukatar ganin an kawo karshen matsalar gawayi, iskar gas da kanfanonin hakar mai ke samarwa .
“Duniyarmu tana cikin mawuyacin hali kuma babban abin da ya haifar da shi shine albarkatun mai, wato gawayi, da iskar gas daga kanfanonin dake hakar mai.
“Kamfanin man fetur na burbushin mai yana da alhakin kashi 86 cikin dari na dukkanin hayaki na C02 a cikin shekaru goma da suka gabata, yayin da suke haifar da tsarin tattalin arziki mai lalata da ke cutar da mutane da kuma duniya. kimiyya ta bayyana a fili, abin da duniya ke bukata a yanzu shi ne kyakyawan yanayi da gaggawa . Bukata ita ce canzawa zuwa tsarin makamashi da tattalin arziki mai inganci,da adalci ga duniya baki daya.
“Tsarin da ya dogara da tushen makamashi mai tsabta kuma ana samarwa tare da mutunta yanayi da kuma haƙƙin ‘yan asalin ƙasar. A duk faɗin duniya, mutane suna yaƙi da masana’antar mai, muna yin tsayayya da haɓaka sabbin bututun mai, ma’adinai da ababen more rayuwa.
“Muna kuma neman hukumomin kudi su daina ba da tallafin man fetur, muna kuma son a dora wa manyan kamfanonin mai da kwal da iskar gas da su biya harajin su,” in ji shi.
Ya ce kungiyar za ta shirya wani taron kade-kade na wake-wake na yanayi a ranar 17 ga watan Satumba, domin fitar da bukatun ta na kawar da burbushin mai tare da maye gurbinsu da hanyoyin samar da makamashi.
Ya kara da cewa hakan zai kare muhalli daga gurbacewar yanayi da yawan amfani da su.
NAN / Ladan Nasidi
Leave a Reply