Take a fresh look at your lifestyle.

Zan Maida Hankali Wajen Bunkasa Rayuwar Mata da Matasa – Hon El-Rufai

Abdulkarim Rabiu, Abuja.

0 174

Dan majaliar tarayyar dake wakiltar mazabar Kaduna ta arewa, Hon Muhammad Bello El-Rufai ya jaddada aniyarsa ta maida hankali wajen bunkasa rayuwar mata da matasa.
Dan Majalisar ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manenema labarai a ofishinsa dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Hon. El-Rufai ya ce akwai shirye-shirye da dama da ya samar domin koya wa matasasa sanaoi kamar su hada takalma, gyaran famfo, aikin kafinta da dai sauransu, sannan za a kara fadada shirin.
Saidai babban kalubalen da ya fuskanta shi ne matasan sun fi so su yi aikin gwamnati.
Ya ce yana kuma da wani shiri na tallafawa mata domin yin sanaoi wanda za a fara kwanannan.
“Za mu dauki wasu mata a kowace unguwa mu basu Naira 100, 000 domin yin sanaa ta yadda za su koyawa wusu dake karkashinsu, idan waina kike yi ki dauki wata ki koya mata”. In ji Hon Bello El-Rufai
Akwai kuma wani shiri na baiwa mata tallafin Naira 10,000 a duka gundumomin dake karkashin mazarmu wanda yanzu haka an fara bayarwa a gundumomin guda hudu.
Dan majalisar yace zai fi maida hankali wajen bai wa al’ummar mazabarsa jari ta yadda za su tsaya da kafafunsu har ma su taimaki wasu a maimakon yin aikin gwamnati.
Ya kara da cewa zai yi kokari na samar da ayyukan gwamnati ga al’ummar mazabarsa batare da banbancin jamiyya, addini ko kabilanci ba.
“idan lokacin bada aiki ya zo, zan kafa kwamiti na musanman wanda zai rika zakulo marasa aikin yi a duka gundumominu, ba zan ba yanuwana ba, ba zan boye wa kowa ba, zan ce a je gidan wane a dauka”.  In ji shi
Sai dai ya gargadi matasan cewa su maida hankali kan sanaoi a maimakon yin aiki gwamnati domin acerwarsa gwamnati ba za ta iya bai wa ko wa aiki ba.
Dangane da halin da ake ciki na kuncin yaruwa sakamakon cire tallafin mai kuwa, Hon Bello El-Rufai ya ce yana nan yana shiri na tallafawa alummar mazabarsa da kayan abinci da suka hada da shinkafa da masara domin rage radadin rayuwa da janye tallafin man ya haifar.
Daga karshe ya yi albishirin cewa zai yi amfani da damar da ya samu na shugabancin kwamitin kula da bankuna don ganin ya taimaki al’ummar mazabarsa, ya kara da cewa yana nan yana fidda tsari domin tallafawa alummarsa musanman mata da matasa.

Abdulkarim Rabiu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *