Take a fresh look at your lifestyle.

Babbar Kungiyar Adawar Masar Za Ta Kauracewa Zabe

Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

0 17

Babbar kungiyar ‘yan adawa ta masu sassaucin ra’ayi a Masar ta ce ba za ta tsayar da dan takara a zaben shugaban kasa da za a yi badi ba bayan da aka yanke wa daya daga cikin shugabanninta hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.

 

 

Kungiyar ta Free Current ta ce Hisham Kassem ya kasance dan takarar shugaban kasa. An same shi da laifin batanci da kuma zagin dan sanda.

 

 

Magoya bayan shi sun ce zargin siyasa ne.

 

 

Ana sa ran shugaba Abdul Fattah al-Sisi zai sanar da cewa zai tsaya takara a karo na uku, amma har yanzu bai yi hakan ba.

 

 

Mutum daya tilo da ya sanar da takararsa ya zuwa yanzu, Ahmed al-Tantawi, ya ce tawagarsa na fuskantar karin tsangwama daga jami’an tsaro.

 

 

BBC/Maimuna Kassim Tukur,Abuja.

Leave A Reply

Your email address will not be published.