Take a fresh look at your lifestyle.

KUNGIYAR DILLALAN MAI TA NAJERIYA IPMAN TAYI BARAZANAR SHIGA YAJIN AIKI

Tijjani Usman Bello

0 316

Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya IPMAN na Jihohin Borno da

Yobe, Alhaji Muhammad Kuluwu, ya sanar da matsalolin da kungiyar ta fuskanta sakamakon rashin biyan bashin da suke bin gwamnati.

 

 

Alhaji Muhammad Kuluwu, ya yi nuni da cewar “A bisa la’akari da bashin da muke bin Gwamnatin Tarayya har sama Naira Biliyan 70, na Kudin Dako, a cikin Shekara guda, bata biyamu ba ya sanyamu durkushewa a yanzu haka bamu iya hassala komai a cikin wannan Sana’atamu, duk wadansu a cikinmu sun fara barin Sana’ar suna komawa wasu harkokin na daban don faduwar da mukeyi bama cin riba, shiko ko wani sana’a anayine don a ci Riba amma ba faduwaba.”

 

 

Shugaban ya kara da cewar” Shi wannan bashin da muke bin Gwamnatin Tarayya har sama da Naira Biliyan 70, cikin Shekara guda to Naira Biliyan Biyu kawai ta dauka ta biyamu a tsakanin Mambobinmu sama da Dubu 2 , a wannan Yanki namu na Jihohin Arewa.”

 

 

 

Yace wannan Yajin Aikin gargadin na tsawon kwanaki 3, da zai fara ranar Talatan nan zasu yi shine da Nufin Jan Kunni ga gwamnati ta biyamu wannan bashi da suke bi cikin Wata guda Kacal, idan kuma bata biyaba to zasu Tsunduma cikin Yajin Aikin da Sai Baba Ta gani, domin zasu dakatar da Dakon Man Fetur din a dukkannin Depo–Depo na Ma a Yankin Jihohin Arewa, musanmma a Tashoshin Dakon Man Fetur din na Garuruwan Maiduguri, Yola, Kano, Gusau,  Jos, Suleja, Kaduna, Gombe, da kuma garin Mina.

 

 

A nasa bayani Bubban Jami’i a Kungiyar Dillalan Man Fetur din ta IPMAN, Alhaji Abdulkadir Mustapha, ya fada cewar” Mun yanke Shawarar Tsunduma wannan Yajin Aikin gargadinne na tsawon kwanaki 3, bayan gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a Otel din PORTO  GULF dake Kano, a ranar 17 ga Watan Agustan wannan Shekarar, na cewar idan Gwamnatin bata biya mana wannan Bashin da muke binta har na Naira Biliyan 70, zamu tsunduma cikin Yajin Aikin gargadi na kwanaki 3, sa’annan idan bata biyamana bukatarmuba har tsawon Wata guda to zamu tafi na gama gari.” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *