Shugaban kasa Muhammadu Buhari a madadin ‘yan kasar da gwamnatin Najeriya, ya taya sabuwar fara ministar kasar Birtaniya, liz truss murna samun wannan mukami da aka amince da ita.
Shugaban ya yi farin ciki da tsohon sakataren harkokin waje na kungiyar kasashe renon Ingila, commonwealth da kuma ci gaban day a samar wa Burtaniya, siyasa da diflomasiyya wadanda suka kara inganta tare da karfafa dangantaka da Najeriya da sauran kasashe.
Ya tabbatar da cewa, dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya ta kasance mai karfi, mai kyau da kuma moriyar juna, yayin da yake aiki tare da fira Ministar liz Truss don zurfafa dagantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Buhari ya yaba da irin soyayya da abokantaka na tsohon fara minista,Boris Johnson, yana yi masa fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba.
Leave a Reply