Take a fresh look at your lifestyle.

Kame Mafi Girma: Brazil Ta Kama Ton 3.6 Na Hodar Ibilis

0 190

Rundunar sojin ruwan Brazil ta ce ta kama wani kwale-kwale na hodar ibilis mai nauyin metric ton 3.6 a gabar tekun jihar Pernambuco da ke arewa maso gabashin kasar, a wani hari mafi girma da Brazil ta kama a gabar tekun kasar.

 

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ruwa ta fitar ta ce ta kama wani karamin kwale-kwalen da ake amfani da shi wajen jigilar mutane da kaya a gabar teku tare da ma’aikatansa biyar da ke kan hanyar zuwa Afirka. Jirgin sintiri ya ja jirgin zuwa tashar jiragen ruwa na Recife.

 

Kame ya biyo bayan jerin ayyukan da sojojin ruwan kasar suka gudanar domin yaki da safarar miyagun kwayoyi a gabar tekun kasar.

 

A cewar rundunar sojin ruwa, sama da tan 17 na hodar iblis, tan 4.3 na hashish, tan 695 na taba sigari, tan 113.34 na kifi, tan 14 na marijuana da kuma cubic meters 3,146 na itace tun daga shekarar 2020.

 

 

 

REUTERS/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *