Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya ce zai sake tsayawa takara a karo na hudu a zaben shugaban kasar da za a yi a shekara mai zuwa.
“Eh, ni dan takara ne,” in ji Mista Kagame a ranar Talata.
Da aka tambaye shi kan abin da kasashen Yamma za su yi game da shawararsa ta sake tsayawa takara, Mista Kagame ya ce, “Na yi hakuri da kasashen Yamma, amma abin da kasashen Yamma ke tunanin ba shi ne matsalata ba”.
“Na yi farin ciki da kwarin gwiwar da ‘yan Ruwanda ke da shi a kaina. Kullum zan yi musu hidima, gwargwadon yadda zan iya.”
A watan Afrilu ne dai Mista Kagame ya ce yana fatan yin murabus tare da mika mulki bayan shafe shekaru 23 yana mulki.
Jam’iyya mai mulki ta kasar Rwandan Patriotic Front (RPF-Inkotanyi), ta rike Mista Kagame a matsayin shugabanta a watan Afrilu. Tun 1998 ya jagoranci jam’iyyar.
Mista Kagame ya kasance shugaban kasar ta gabashin Afirka tun shekara ta 2000. Kuri’ar raba gardama mai cike da cece-kuce a shekara ta 2015 ta kawar da kayyade wa’adi biyu na kundin tsarin mulkin kasar.
Ya lashe zaben da ya gabata a shekarar 2017 da kashi 98.8% na kuri’un da aka kada.
Kasar Rwanda karkashin shugaba Kagame ta samu kwanciyar hankali a siyasance amma masu suka da kungiyoyin kare hakkin bil adama na zargin gwamnatinsa da takaita ‘yancin siyasa da kuma murkushe ‘yan adawa.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply