An dakatar da Gabon a wani bangare daga kungiyar Commonwealth bayan da kwamandojin soji suka yi juyin mulkin da ya hambare shugaba Ali Bongo.
Ministocin harkokin wajen kasashen renon Ingila ne suka yanke wannan shawara a kan gabar babban taron Majalisar Dinkin Duniya.
Shugabannin sun yi kira ga Gabon da ta kiyaye dabi’u da ka’idojin kungiyar Commonwealth.
Sun bukaci kasar da ta gudanar da sahihin zabe cikin gaggawa.
Sojojin Gabon sun hambarar da Mista Bongo daga mulki jim kadan bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Mista Bongo dai ya kasance kan karagar mulki a kasar mai arzikin man fetur tun shekarar 2009, lokacin da ya gaji mahaifinsa da ya shafe shekaru 41 yana mulkin kasar.
Da farko dai an tsare shi a gidan yari yayin da shugabannin sojoji suka karbe ragamar mulki, amma daga baya aka sake shi aka ba shi izinin tafiya kasashen waje domin a duba lafiyarsa.
Ministocin harkokin wajen -da ke zaune a matsayin kungiyar ministocin Commonwealth – sun bukaci kasar Gabon ta ba da tabbacin tsaron lafiyar Mista Bongo da na iyalansa, kuma a cikin wata sanarwa da suka fitar sun ce “sun yi Allah-wadai da matakin tsige zababben gwamnati daga mukaminsa ba bisa ka’ida ba”.
Sun ce dakatarwar ta Gabon tana nan “har sai an maido da mulkin dimokradiyya”. Ta kebe Gabon daga dukkan tarurrukan gwamnatocin kasashen Commonwealth da suka hada da ministoci da shugabannin tarurrukan gwamnati.
An nada sabon firaminista Raymond Ndong Sima a matsayin firaminista na wucin gadi a watan Satumba, bayan da Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa Mr Bongo, ya zama shugaban rikon kwarya na Gabon.
Da yake magana kwanan nan, Mista Sima ya ce ya kamata kasar ta sake gudanar da sabon zabe nan da shekaru biyu.
Ministocin Commonwealth sun ba wa sabbin shugabannin Gabon shekaru biyu daga 30 ga Agusta 2023 don gudanar da sahihin zabe. A cikin sanarwar sun kara da cewa idan ba a samu ci gaba a wannan lokaci ba, za a iya cire kasar daga kungiyar baki daya.
Duk da yin Allah wadai da juyin mulkin da wasu shugabannin kasashen Afirka da na yammacin duniya suka yi, da alama fararen hula sun yi maraba da wannan sauyin.
Da yawa daga cikin ‘yan kasar Gabon sun nuna shakku kan matakin Mr Bongo na tsayawa takara karo na uku. Ya fara hawan karagar mulki ne a zabe shekaru 14 da suka gabata bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo, wanda ya shafe fiye da shekaru 40 ke mulkin kasar.
Wasu kuma sun nuna shakku sosai game da iya aikin shi na samar da ingantaccen jagoranci, bayan da ya yi fama da hawan jini a watan Oktoban 2018.
BBC/Ladan Nasidi.
Leave a Reply