Somaliya na neman tsaikon janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a kasar.
Kasar ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta jinkirta da watanni uku a zango na gaba na ficewa daga dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka a Somalia (ATMIS).
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato wata wasika da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar ta Somalia Hussein Sheikh-Ali ya rubuta wa Majalisar Dinkin Duniya yana cewa “Somaliya ta bukaci a dakatar da aiki a hukumance a cikin shirin rage yawan ma’aikatan ATMIS 3,000.
Dakaru 3,000 daga cikin dakaru 17,000 ne ya kamata su bar kasar nan da karshen wata a mataki na biyu na janyewar.
Sai dai gwamnatin Somaliya, wacce a halin yanzu take yaki da mayakan al-Shabab, ta ce tana fuskantar koma baya.
Kudiri da Majalisar Dinkin Duniya ta zartar sun bukaci janye dakarun ATMIS gaba daya nan da karshen shekara mai zuwa tare da mikawa sojojin kasar Somaliya cikakken alhakin tabbatar da tsaro.
Rundunar ta fara janye dakarun ta sannu a hankali a watan Yuni.
BBC/ Ladan Nasidi.
Leave a Reply