Shugaban kasar Mozambique Filipe Jacinto Nyusi ya samu tarba daga sakataren tsaron Amurka inda suka tattauna dangantakar tsaron kasashen biyu da hadin gwiwar tsaro.
Tun a shekarar 2017, lardin Cabo Delgado da ke arewacin Mozambique, ke fama da rikici tsakanin hukumomi da mayaka masu tsattsauran ra’ayi.
Austin ya bayyana aniyar yin aiki tare da Mozambique “don kawar da musabbabin rikici da fadada tsaro a yankin.”
“Ta’addanci ya kasance babbar barazana ga tsaron yankin. Kuma kasashen mu biyu sun sha fama da ta’addanci. Kuma muna cikin wannan tare. Don haka muna matukar godiya da hadin gwiwar da kuke yi na yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a arewacin Mozambique da hadin gwiwar da kuke yi da kungiyar raya kasashen kudancin Afirka, Tarayyar Turai da sauran su na nuna karfin hadin gwiwa wajen yakar ta’addanci.”
“Ina so in gode muku da gaske da kuma Shugaba Biden da gwamnatin Amurka saboda goyon bayan da muke samu a fannoni daban-daban da suka hada da tattalin arziki, lafiya, da tsaro.”
Shugaba Filipe Nyusi da Lloyd J. Austin III, wadanda suka gana a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, sun kuma yi musayar ra’ayi kan wayar da kan yanki da karfafa tsaron teku.
Africanews/Ladan Nasidi.
Leave a Reply