Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin Ceton Daliban Jami’a Mata

0 120

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumomin tsaro da su yi kokarin kubutar da sauran daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara, wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a baya-bayan nan.

Shugaban ya ba da umarnin ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Cif Ajuri Ngelale.

Yayin da yake nuna rashin amincewa da wannan abin kyama na sace mutane, shugaban ya ci gaba da cewa babu wani dalili na da’a da zai iya tabbatar da irin wannan danyen aiki da aka yi wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba, wadanda laifinsu kawai shi ne neman ilimi mai kyau.

Yayin da shugaban ke mika ta’aziyyarsa ga dukkan iyalan da lamarin ya shafa kai tsaye, ya jaddada cewa gwamnatinsa tana da alhakin kare duk wani dan Najeriya.

Shugaban ya ci gaba da cewa, bisa jajircewar sa, ya baiwa iyalan daliban da aka sace tabbacin daukar duk wani mataki na ganin an sake haduwa da su cikin koshin lafiya.

Bugu da kari, shugaban ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi sun kasance wuraren ilimi, ci gaba da dama, kuma sun kubuta daga munanan ayyukan ta’addanci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *