Take a fresh look at your lifestyle.

Karamar Ministar Abuja Tayi Alkawarin Kyautata Ma’amala Ga Masu Zuba Jari Na Kasashen Waje

0 113

Hukumar da ke Kula da Babban Birnin Tarayya, FCTA, ta tabbatar wa masu zuba jari na kasashen waje da ke da sha’awar zuba jari a babban birnin kasar nan, da zasu samu damar yin hakan.

Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya (FCT) Dr Mariya Mahmoud wacce ta wakilci Ministan Babban Nirnin Tarayya, Barista Nyesom Wike, ta bayyana haka a taron baje kolin kasuwancin kasa da kasa na Afirka da aka kammala a Midtown, New York, kasar Amurka.

Dakta Mahmoud ya ce a ko da yaushe Gwamnatin za ta samar da matakan da za su samar da ingantattun shirye-shirye da tsare-tsare na tattalin arziki da za su samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ga masu zuba jari.

Ta zayyana manyan wuraren da gwamnati da mazauna yankin ke bukata da suka hada da Noma, yawon bude ido, samar da ababen more rayuwa, sufuri, kiwon lafiya, sarrafa shara da kuma sana’ar karbar baki. Ta bayyana cewa halartar FCTA a taron zuba jari ya kara bude wasu damammaki na zuba jari kai tsaye na kasashen waje (FDI) zuwa yankin.

Ministan ya ce Kamfanin zuba jari na Abuja Limited da Abuja Infrastructure Investment Centre ne za su jagoranci shirin domin aiwatarwa cikin sauki.

A cewarta; “Shigowar gwamnati a taron zuba jari na da matukar muhimmanci. Taron ya ba mu damar gabatar da damar zuba jari a FCT, da kuma babbar dama don yin magana game da yuwuwar a fannin noma.

“Wannan dandali ne na kira ga jama’armu, musamman wadanda ke kasashen waje, da su shigo cikin jirgin, su taimaka mana wajen magance matsalar karancin abinci.

“Sannan muna da yawon bude ido, samar da ababen more rayuwa, sufuri, da kiwon lafiya, sarrafa sharar gida da masana’antar karbar baki. Duk wadannan wurare ne da mutane za su iya zuwa su zuba jari. Kuma hakika muna bukatar hadin kai da hadin gwiwar jama’a domin idan ba tare da hadin gwiwa ba, ba za mu iya cimma abin da muke son cimmawa ba”.

Mahmoud, ya kuma yi amfani da dandalin wajen neman zuba jari mai yawa a gidaje masu rahusa, inda ya yi nuni da cewa, Gwamnati a shirye take ta inganta zamantakewar al’umma da tattalin arziƙin jama’a, bisa la’akari da sabbin tsare-tsare na wannan gwamnati.

Taron ya kasance mai taken: “Wajibi ne na kasuwanci a duniya ga masu kananan sana’o’i na Afirka a matsayin mai sauya wasa ga ci gaban nahiyar”.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *