Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Karamar Hukumar Borgu A Jihar Neja Ya Taya Yan Najeriya Murnar Cika Shekaru 63

By Nura Mohammed, Minna

0 154

Shugaban Karamar Hukumar Borgu dake jihar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya Alhaji Sulaiman Yarima ya bukaci alummar jihar da ma kasa baki daya da su kasance Yan uwan juna da samar da hadin Kai a tsakankanin su domin ganin kasar ta sami ci gaba mai daurewa.

Alhaji Sulaiman Yarima ya bukaci hakan ne a zantawar sa da manema labarai a garin Minna fadar gwamnatin jihar Neja, domin taya alummar kasar cika shekaru 63 da samun ‘yan cin kai daga turawar mulkin Ingila a shekara ta 1960.

Shugaban karamar hukumar ya ce yana kwarin gwiwar gwamnatin mai ci na Shugaba Bola Ahamad Tunubu zata kawo ayyukan cigaba ga alummar kasar, duba ga irin tsare tsaren ta da kuma yadda ta shirya samarwa da alumma cigaba ta fanin tattalin arziki da inganta bangaran tsaro da sauran batutuwa na cigaba.

Alhaji Sulaiman Yarima ya kara da cewar Gwamna Umar Mohammed Bago bisa ma’aunin yadda ya bijiro da ayyukan cigaba a jihar Neja alumma zasu sharbi romon mulkin sa , inda ya bukaci sauran shugabannin kananana hukumomi dake fadin jihar da su hada hannu da gwamnatin wajan ciyar da jihar Neja gaba.

Ya kuma bukaci alummar jihar da ma kasa baki daya da a cigaba da yin addu’oin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma nemama kasa samun cigaba mai daurewa, inda ya ce gwamnatin Jihar da na taraya na kokarin ganin sun kawo karshen matsalar tsaro, da kuma inganta bangaran Noma ta yadda rayuwa zata koma kamar da.

Zaman lafiya shine kashin cigaban kowance alumma, a don haka akwai bukatar ganin mun cigaba da yiwa jiha da ma kasa Baki Daya addu’oi.” in ji Sulaiman Yarima.

A karshen ya yabawa alumma musammama ‘yan asalin jihar Neja bisa irin goyan baya da suke baiwa gwamnatin mai girma Gwamna Umar Muhammad Bago domin ganin ta shinfida masu ayyukan cigaba da zai taba rayuwar su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *